Ingantaccan Tsarin Abinci (Hausa) Sursa de nutriție Harvard T

hausa

Ingantaccen tsarin abinci, wanda kwararru kan kimiyyar abinci na sashen lafiyar al'umma da ke jami'ar Harvard tare da masu tace dab'in kiwon lafiya na Harvard suka kirkiro, wani jagora ne na samar da ingantacce kuma lafiyyen abinci faranti ne ko kwanon aka iya are a tafi da shi. A saka kwafi a jikin firinji a matsayin matashiyar samar da abinci mai gina jiki.

  • Mafi yawan abincin ka ya zama ganyayyaki ne da ‘ya’yan itace - ½ na kwanon ka:

Ka lura da launi da kuma nau’I kuma a kiyaye cewa dangogin dankali basa daga cikin ganyayyaki a tsarin ingantaccen abinci saboda rashin kyan tasirin su a cikin jini.

  • Zabi zallar hatsi - ¼ na kwanon ka:

Zallar hatsi marar sirki - kamar alkama dawa jar shinkafa da sauran dangin su da kuma abincin da aka samar daga garesu kamar taliyar alkama na da saukin illa ga sugan dake cikin jini da kuma sinadarin da ke sarrafa shi wanda ake kira (insulin) fiye da farin biredi ko farar shinkafa da sauran nau'I na hatsin da aka surfe shi aka kuma sarrafa shi.

  • Abinci mai gina jiki - ¼ na kwanon ka:

Kifi, kaji, wake da irin su gyada da gurjiya duka hanyoyi ne da ake samun lafiyayye kuma ingantaccen abinci mai gina jiki - ana gauraya su a cikin salak kuma suna haduwa yadda ya kamata da sauran ganyayyaki a cikin abinci. A takaita cin naman dabbobi da ake kira jan nama kuma a kaucewa naman da aka riga aka sarrafa shi kamar malkadadden naman gwangwani da ake kira a turance “bacon” da kuma “sausage”.